Kamfanin man fetur na kasa,NNPCL ya dakatar da sayarwa da ‘yan kasuwar man fetur karkashin kungiyar IPMAN da mai.
Hakan na zuwane bayan da kamfanin man ya kara farashin man fetur din a gidajen man su zuwa akalla Farashin Naira 855 har zuwa sama.
Wakilin kungiyar na IPMAN, Hammed Fashola ya bayyana rashin jin dadi kan lamarin inda yace aun biya kudin sayen man fetur din amma gwamnati ta dakatar da komai.
Ya bayyana cewa basu dan dalilin yin hakan ba dan kuwa zuwa yanzu NNPCL bata gaya musu me ya kawo dakatar da sayar musu da man fetur din ba.