Nabil Shinkafi Ya Zama Shugaban Matasan Arewa
Manyan kungiyoyin Arewacin Nijeriya masu zaman kansu, sun tabbatar da shugabancin Matashin ɗan kasuwa Nabil Shinkafi, a matsayin Shugaban Matasan Arewa, inda suka bashi takardar shedar shugabanci (Certificate) kuma sun karrama shi da Numbar yabo.
Manyan kungiyoyin Matasan Arewa Youth Leadership groups sun karrama matashin ɗan kasuwar Nabil Shinkafi a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagorori masu son ci gaban mutanen Arewacin Nijeriya, ta hanyar samar masu da abin yi; da kuma inganta iliminsu.
An yi taron karrama matashin a jiya Talata, a babban birnin tarayya Abuja.