Babban Alkalin Najeriya, Olukayode Ariwoola ya kira Alkalin babbar kotun tarayya dake Kano da alkalin babbar kotun jihar Kano kan Shari’ar masarautar Kano.
Babbar kotun tarayya dake da zama a Kano ta bayar da umarnin sauke Muhammad Sanusi II daga kan kujerar sarautar Kano inda tace a mayar da sarki Aminu Ado Bayero.
Saidai ita kuma babbar kotun Kano ta tabbatar da Sarki Muhammad Sanusi II a matsayin sarkin Kano inda tace a fitar da Sarki Aminu Ado Bayero daga Masarautar Nasarawa da yake zaune.
Wannan lamari ya kawo rudani sosai inda aka rasa wane hukunci za’a yiwa biyayya.
Babban alkalin na kasa ya kirasu alkalan Kanon ne inda yace zasu zauna dan tantance hurumin kowace kotu da kuma tabbatar da aka yin hukunci na bai daya.
Sannan kuma Sanarwar tace za’a yi kokarin ganin irin hakan bata sake faruwa ba nan gaba.