Monday, December 16
Shadow

TSADAR KUDIN MOTA: Ɗan Agajin Izala Ya Yi Tafiyar Kilomita 161 Da Keke Domin Halartar Wa’azin Ƙasa A Jihar Adamawa

Muhammad Ɗan Liti Dan Agajin izala reshen Jos da ya taso daga karamar hukumar Maiha zuwa Jimeta domin halartar wa’azin ƙasa wanda ya gudana a jiya Asabar.

Dan Agajin ya taso ne tun a ranar alhamis ɗin data gabata ne da keken sa, wanda ya ya yadda zango a garin gombi domin hutu da cin abinci.

Matashin ya bayyana cewa “ya iso cikin garin Jimeta ne a jiya a Asabar, ya kuma ƙara da cewa ya yi wannan tafiyar ne saboda yanayin da ake ciki na tsadar kuɗin mota”.

Domin idan a mota ne zan kashe kuɗin da bai gaza 15,000 ba kuma bani dasu a hakan yasa nayi amfani da abinda nake dashi domin halartar wannan wa’azi.

Karanta Wannan  Mutane 10 sun mùtù da dama sun jikkata a mummunan hadarin mota da ya faru a jihar Jigawa

Babban abinda ya sa ni zuwa wannan wa’azi shine inada buƙatar sake sayan wasu kayyaki na kayan agaji da kuma sauraren wa’azi, daga cikin kayayyakin da ya ambata a ciki akwai hula da kuma bell, inji shi.

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *