Tauraron mawakin Kudu, Davido yayi murnar zagayowar ranar haihuwarsa inda ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta.
Saidai a wannan karin ya zo da sabon salo ba wanda aka saba gani ba a baya.
Davido ya bayyana cewa +1 Alhamdulillah.
Hakan yasa mutane ke ta tambayar shin ko dai Davido din ya musulunta ne?