Taliya da doya cimace da ake yi musamman a kasar Hausa duk da yake ba kowane ya iya wannan dahuwa ba.
Ga Yanda zaki Dafa Taliya da Doya:
Dahuwar Taliya da doya fara:
Zaki samu Tukunya me kyau a zuba ruwa kofi 4. A Dora a wuta.
A yayin da kike jiran Ruwan ya tafasa, sai ki fere doyar sanda daya ki sakata cikin ruwa me kyau. Ruwan na tafasa sai ki saka doyar ita kasai.
Idan ta kai mintuna 5 zuwa 8 haka sai ki zuba taliyar. Bayan mintuna 15 zuwa 20 ya isa ace sun dahu.
Sai a sauke.
Ana iya ci da miya ko da mai da yaji ko kuma da wani abu daban da ake so.
Dahuwar Taliya da Doya Jollof:
Idan kuwa Jollof ne za’a yi sai a tanadi:
Kayan Miya a markado ko a samu na leda.
A tanadi albasa.
A tanadi magi.
A tanadi doyar da taliyar.
A tanadi farin mai ko man ja, ya danganta wanda ake so.
A tanadi kifi, ko nama ya danganta wanda ake so.
A tabadi Karas in da hali.
A dora tukunya a zuba mai a saka nama ko kifi da aka tanada a yanka Albasa a soyasu da kyau. Bayan sun soyu sai a zuba kayan miyan da aka tanada.
Bayan Mintuna 5 sai a zuba ruwa kofi 4.
Idan ruwan ya tafasa sai a zuba doya, a barta ta dahu zuwa mintuna 5 haka, sai itama taliyar a zubata a barsu zuwa mintuna 15.
A bude a yanka Albasa, A yanka karas, a zuba magi a jiya sosai, a rage wuta a barshi zuwaintuna 5 a sauke a ci.