JOLLOF DIN SHINKAFA ME DADDAWA
Shinkafa,
jajjagen kayan miya
Maggi,
daddawa,
mai
Ruwa
nama
daddawa,
mai
YADDA AKE HADAWA
Da farko zaki gyaran kayan miyanki,tumatir kadan,attarugu,tattasai,albasa,tafarnuwa,ki wanke ki nika/jajjaga
Ki dora tukunyarki kan wuta,ki zuba mai,kisa yankakkar albasa idan yadanyi laushi kizuba tafasashen namanki,ki soya naman sama sama
Idan yadayi ja,seki zuba jajjagen/nikakkun kayan miyanki,ki soya har su soyu,idan suka soyu ki zuba ruwan da ze iya dafa miki shinkafanki.
Bayan kin zuba ruwan,ki zuba daddawanki dai dai yawan yanda kikeson kamshinta da gardinta ya fito miki a jolof dinki
Kizuba maggi,da Dan gishiri kadan ki rufe har ruwan ya tafasa ki wanke shinkafarki ki zuba ki motsa sai ki rufe da mirfi
Idan shinkafan yakusa nuna ki rage wuta kisaka foil papper ki dora murfi akai domin ya sulala
Wannan shinkafan yanada dadi sosai,kedai ki gwada zaki bamu labari.