Bidiyo ya bayyana da ya nuna yanda ake ta kokarin gyara wutar lantarkin Arewa data lalace.
Yau Kwanaki 10 kenan cif ba wutar lantarki a Arewa bayan da wasu bata gari suka lalata wutar.
Lamarin ya jefa jihohi da yawa a yankin cikin duhu sannan ya sanya mutane da yawa tafka asara ta miliyoyin kudade a wasu Rahotannin ma har rayuwa an rasa.
Hukumar TCN dai tace ranar Lahadi 3 ga watan Nuwamba za’a kammala gyaran wutar lantarkin.