Hadimin shugaban kasa dake bashi shawara akan harkar sadarwa da wayar da kan al’umma, Sunday Dare ya bayyana cewa kamata yayi a yabi shugaban kasar, Bola Ahmad Tinubu akan cire tallafin man fetur.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV inda yace shuwagabannin kasashe da aka yi a baya da yawa sun kasa cirewa sai shine yayi namijin kokari ya cire tallafin man fetur din sannan ya kuma cire tallafin dala.
Yace wasu kalilan ne a kasarnan ke samu makudan kudade da tallafin wanda ke sa gwamnati na tafka mummunar asara.
Cire tallafin dai ya sanya farashin man fetur ya tashi daga sama da Naira 200 akan kowace lita zuwa sama da Naira 1000 akan kowace lita kuma man fetur ne hanyar da ‘yan Najeriya ke amfani da ita wajan samun makamashi a gidajensu da wajen kasuwancinsu.
Lamarin cire tallafin man fetur din dai yasa da yawa sun kulle kasuwancinsu wasu kuma sun tafka mummunar asara.