Daya daga cikin lauyoyin dake baiwa yaran da gwammatin tarayya ta kama bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu ta hanyar zanga-zanga watau Deji Adeyanju ya bayyana cewa, basu san inda yara 2 daga cikin yaran da gwamnatin tarayyar ta kama auke ba.
Yace yaran biyun ya kamata ace an gurfanar dasu a gaban kotu tare da sauran yara 32 da aka kai kotu ranar Juma’ar data gabata.
Saidai yace zuwa yanzu basu san inda yaran suke ba kuma basu san abinda ya faru dasu ba.
Ya bayyana hakane a wata hira da jaridar Punch ta yi dashi.