Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya mayarwa Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar martani kan sukar da ya masa game da yanda yake gudanar da mulki musamman ma hanyar da ya bi wajan cire tallafin man fetur.
Atiku ya baiwa Tinubu shawarar ya dauki tsare-tsaren da yaso yayi da yaci mulki dan su taimaka masa ya fitar da ‘yan Najeriya daga halin kunci.
Saidai a martaninsa ta bakin me magana da yawunsa, Bayo Onanuga, shugaba Tinubu yace ai ‘yan Najeriya sun bayyanawa Atiku cewa basa son tsare-tsarensa tunda suka ki zabensa a matsayin shugaban kasa.
Yace Kuma bai san irin kwamacalar da ya iske bane akan mulki da ba zai rika sukarsa haka ba, yace abubuwan da ya iske dolene ne tasa sai ya cire tallafin man gaba daya.
Yace kuma Atikun da mai gidansa Obasanjo sun samu damar yin duk gyare-gyaren da ya kamata su yiwa kasarnan amma basu yi ba.
Saidai Tinubu yace ya yadda da Atiku a bangaren da yake kiranshi da ya tausayawa ‘yan kasa, yace kuma yana yin hakan.