Dan takarar shugaban kasa a jami’iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa ko da ya kama matarsa tana cin amanarsa da wani namiji ba zai sake ta ba.
Peter Obi ya bayyana cewa aminci da soyayyar dake tsakaninsa da matarsa abune me karfi sosai.
Peter Obi yace ko da za’a harbeshi da Bindiga ko ya kamata tana cin amanarsa da wani namiji ba zai iya rabuwa da ita ba.
Peter Obi yace matarsa idan ta ga dama ta aikata duk abinda take so shidai ba zai iya rabuwa da ita ba.
Peter Obi dai da matarsa, Margaret Brownson sun shafe shekaru 30 da aure.