An ga wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta inda aka ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya baiwa Tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso kujerar da yake zaune dan ya zauna.
Hakan na zuwane yayin da rahotanni ke yawo cewa an samu baraka a tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwankwason.
A jiya dai hutudole ya kawo muku rahoton cewa, Jaridar Daily Nigerian tace Abba ya daina daukar wayar Kwankwaso.