Dan jarida me binciken kwakwaf, Fisayo Soyombo ya zargi hukumar Kwastam da taimakawa masu fasa kwaurin shinkafa zuwa cikin Najeriya.
A bayanan da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce yanzu haka ana sauke shinkafar da aka shigo da ita daga kasar Benin Republic a Lusada dake karamar hukumar Ado Odo/Ota ta jihar Ogun.
Soyombo ya bayyana cewa lamarin na faruwane a ranar Laraba inda yace kuma an sallami duka wani jami’in Kwastam da zai kawo tangarda a lamarin.
Dan jaridar yace sauran shinkafar za’a tafi da ita zuwa Legas.
A baya dama dan jaridar ya bayar da bayanai akan shigowa da shinkafar amma hukumar kwastam ta karyatashi.