Thursday, December 26
Shadow

Hotuna: Wannan bawan Allahn ya tsero daga hannun ‘yan Bìnďìgà a jihar Zamfara bayan kwanaki 47 suna rike dashi

{“remix_data”:[],”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Wannan bawan Allah me suna Salim Ishaq Umar dakw zaune a Gusau Jihar Zamfara ya tsero daga hannun masu garkuwa da mutane da suka saceshi.

Ya tsero ne daga Munhaye inda a canne ‘yan Bindigar suke tsare dashi.

Ya tsero ne ranar 12 ga watan Nuwamba inda kuma bayan ya kai ga sojoji ya nemi su taimaka masa.

Da yake bayar da labarin yanda aka yi garkuwa dashi, yace ranar 8 ga watan Augusta ne lamarin ya faru inda ‘yan Bindigar suka shiga har gida suka kamashi.

Yace sun harbi wani jami’in tsaro sannan kuma shi sun kwace wayar hannunsa.

Ya kara da cewa, sun nemi a bayar da Miliyan 30 kudin fansarsa slda mashina 5 inda danginsa suka bayar. Yace amma suka ki sakinshi inda suka kara yawan kudin da suke nema zuwa miliyan 100 da mashina 10.

Karanta Wannan  TSADAR KUDIN MOTA: Ɗan Agajin Izala Ya Yi Tafiyar Kilomita 161 Da Keke Domin Halartar Wa'azin Ƙasa A Jihar Adamawa

Ya bayyana cewa su 3 ne suka yi yunkurin tserewa amma an sake kama sauran biyun shine kadai ya tsamu ya tsero daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *