Kyan fuska na daya daga cikin abubuwan da Mata ke nema ruwa a jallo sukan kashe makudan kudade wajan gyaran fuskarsu.
Ko da yake a yanzu har maza ma na yin gyaran fuskar saboda zamani.
Ga bayanai dalla-dalla kan yanda za’a yi gyaran fuska da kayan gargajiya na gida.
Maganin Kyan fuska da dankali
Ana cin dankalin Hausa ko a shafashi a fuska dan kyan fuskar da kawar da duk wani datti da duhun fuskar.
Yana kuma maganin takurewar fuska irin na tsufa.
Dan samun wannan armashi, a ci dankalin Hausa ko a rika shafashi a fuskar akai-akai.
Maganin Kyan fuska da Tumatir
Tumatir na daya daga cikin abubuwan da ake amfani dasu wajana gyaran fuska.
Yana maganin tattarewar fuska, idan fuska na yawan yin maiko, Tumatir na maganin hakan, yana kawar da duhun fuska wanda hasken rana ke kawowa.
Tumatir Yana Sanya hasken fuska sosai.
Ana shafa tumatir a fuska ko a ci duka za’a samu wannan abubuwa da muka lissafa.
Ana kuma hadashi da ruwan cucumber ko ace gurji a shafa a fuska a bari ya kai mintuna 20 kamin a wanke da ruwan dumi.
Ana kuma hada Tumatir da ruwan Zuma babban cokali 2 shima Tumatirin a zuba cokali biyu a kwaba a rika shafawa a fuska ana wankewa bayan mintuna 20 da ruwan dumi.
Hakanan anan hada ruwan tumatir Dana lemun tsami da madara a kwaba a shafa a fuska bayan mintuna 20 a wanke da ruwan dumi.
Ayaba ma na gyara Fuska.
Idan ana son kyan fuska sosai, ta yi haske ta rika sheki babu duhu babu kuraje, a dage da cin ayaba kullun.
Hakanan ana iya kwaba ayabar a rika shafata a fuska ana bari tana yin kamar mintuna 20 sai a wanke da ruwan dumi.
Hakan yana kawar da dattin fuska, kuraje, da duhun kasan ido da sauransu.
Hakanan ana hada ayaba da Zuma da ruwan lemun tsami a rika kwabawa ana shafawa fuska shima wannan hadi yana gyara fuska sosai.
Sauran abubuwan dake kawo kyan fuska sun hada da kurkur, man kwakwa, Aloe Vera, da sauransu.