Monday, December 16
Shadow

Abubuwan dake kara dankon soyayya

Kara dankon soyayya tsakanin saurayi da budurwa da kuma mata da miji na da matukar amfani domin kamar shukace da aka yi, ya kamata ana bata ruwa.

Ga abubuwan dake kara dankon soyayya kamar haka:

  1. Kyauta: Kyauta na da ya daga cikin abubuwan dake kawo soyayya da kara mata danko. Ko da mutum baya sonka idan ka fara yi mai kayauta yau da gobe, zai so ka. Kyauta ba dole sai ta kudi ba, ka lura da abinda masoyinka yake so ko kake tunanin zai so ka rika kyautata masa dashi
  2. Kyawawan Kalamai: Kyawawan kalamai ko da ba a soyayya ba abune me kyau, ballantana ga masoya. Ya kamata masoya su rika musayar kyawawan kalamai a tsakaninsu, misali ina sonki, ko ina sonka, kana burgeni, kina burgeni, kina sanyani farin ciki, ban gajiya da kallonki, da dai sauransu.
  3. Yabo: Yabo yana da matukar tasiri wajan kara dankon soyayya, kuma yabon ya kasance na gaskiya ne, ba na wuce gona da iri ba. Misali masoyi ya kamata ya lura da abinda masoyinsa ya kware akansa, iya kwalliyane, kyautace, murmushine, Hakurine, iya girkine, dadai sauransu ya rika yabawa masoyinsa akai, hakan yana kara dankon soyayya.
  4. Tsafta da Kwalliya: Babu Wanda ke son yin tarayya da kazami, Dan haka ya zamana ana kula da tsaftar jiki data kaya, hakanan kwalliya ma na karawa masoyinka ya ji kana kara Shiga ransa.
  5. Banda Mita: Idan aka yi Abu na rashin jituwa ko rashin fahimtar juna ta shiga, aka sasanta, a barshi ya wuce kada a rika tado da maganar lokaci zuwa lokaci, hakan na ragewa mutum kima a gaban masoyi. Hakanan ya zamana cewa kana da kawaici, ba kowace magana Mara dadi bace aka gaya maka kace saika mayar da martani akai ba
  6. A koyi daidaita kishi: Kada kana ganin wani abu da baka fahimta ba tsakanin masoyinka da wani ba kawai ka dauki mataki ba tare da yin bincike ba, ka danne zuciyarka har ka gano gaskiyar lamarin kamin ka dauki mataki.
  7. Barkwanci da Nishadi: Soyayya ake ba kiyayya ba, ya kamata a iya zolaya, tsokana, wasa, da ban dariya, idan hali ya bayar, lokaci zuwa lokaci a dan rika fita yawon shakatawa ana ciye-ciyen kayan makwalashe, irin su tsire, shawarma, Pizza, chocolate, ice cream da sauransu.
Karanta Wannan  Hirar soyayya masu dadi

Namiji ko da baka da abinda zaka baiwa mace, ka rika bata labarin irin rayuwar Jin dadin da kake tsara muku kai da masoyiyarka nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *