Ƴan sanda sun cafke wani mutum a Bauchi da ya yi yunkurin sayar da ‘yarsa Naira milyan ɗaya da rabi (N1.5m)
Magidancin dan shekara 39 mai suna Yusuf Umar da ke kauyen Dagu a karamar hukumar Warji a jihar Bauchi yayi yunkurin $ayar da diyarsa mai shekaru 5 a kan kudi naira miliyan 1.5 bayan sun rabu da mahaifiyar yarinyar,
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Auwal Musa Mohammed ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da gabatar da wanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sandan da ke Bauchi.