Matar tsohon gwamanan jigar Ondo, Rotimi Akeredolu, Betty Akeredolu na fuskantar zargin hannu a mutuwar mijin nata.
Betty dai a baya wadda inyamurace, ta bayyana kabilar Yarbawa da cewa basu da asali saboda yawan zinace-zinace da matan aure da mazajensu ke yi, tace da yawa yaran yarbawa basu san ubanninsu ba.
Wannan magana tawa yarbawa da yawa zafi inda suka yi ta mata raddi.
Ana cikin hakane kuma sai aka sake samun Betty ta mayarwa wani martani da yace mijin nata tsohon me kwakulo kawunan matattu me a kabari, wani zargi da Inyamurai ke yiwa yarbawa saboda yin tsafi.
Dalilin hakane yarbawa da yawa ke neman ya kamata a binciki Betty akan mutuwar mijinta saboda yanda take nuna bata damu ba dan anci zarafinsa.