Jam’iyyar hamayya ta PDP ta bayyana cewa, hirar da ‘yan Jarida suka yi da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta farko tun bayan hawansa mulki a Ranar Litinin ta nuna cewa bai damu da halin da ‘yan Najeriya ke ciki ba.
Me magana da yawun PDP, Debo Ologunagba ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar inda yace maganar da shugaban kasar yayi ta cewa bai yi nadamar cire tallafin man fetur ba ta nuna bai damu da halin da mutane ke ciki ba.
Yace shugaban kasar kamata yayi ya nuna damuwa akan halin da mutane ke ciki da kuma bayyana hanyoyin da zasu dauka dan kawowa mutane sauki.
Yace ba gaskiya bane maganar shugaban kasar ta cewa an samu ci gaba a kasarnan bayan hawan mulkinsa, inda yace mutuwar da aka rika yi wajan turmutsutsu na karbar abincin tallafi alamace dake nuna irin halin kuncin da mutane ke ciki.
Hakanan yace maganar cewa wai tsaro ya samu duk da garkuwa da mutane da ake yi da shugaban kasar ya fada ba haka take ba.
Yace yana baiwa shugaban kasar shawarar ya yi tafiya daga zuwa Legas a mota hakanan ya shiga cikin kasuwanni dan sanin halin da mutane ke ciki.