A kalla Sojoji 6 ne suka jikkata biyo bayan harin da aka kai wa sansaninsu dake Jihar Borno da jirgi marar matuki wanda ake zargin Kungiyar B0k0 Hàràm da kaiwa.
An kai harinne a Wajiroko dake karamar Hukumar Damboa da yammacin ranar Talata.
Waji soja da ya shaida lamarin ya gayawa majiyar Hutudole.com cewa da farko sun ji kamar karar jirgin sama inda daga baya suka ji karan fashewar abubuwa.
Hutudole.com ya fahimci cewa, a baya Kungiyar ta B0K0 Hàràm ta taba kai hari kan sansanin inda suka yi harbin kan mai uwa da wabi wanda daga baya sojojin suka dakile harin.
Wata majiya tace an lalata motar yaki ta sojoji guda 1 a yayin harin.