Tuesday, January 7
Shadow

An kuɓutar da wani yaro bayan kwana biyar tare da zakuna da giwaye

An kuɓutar da wani yaro ɗan shekara takwas, bayan shafe kwana biyar a gandun dajin zakuna da giwaye a arewacin ƙasar Zimbabwe.

Lamarin ya faru ne a lokacin da yaron mai suna Tinotenda Pudu ya yi ta gararamba a cikin gandun daji Matusadona Game Park, kamar yadda ɗan majalisar gabashin yankin Mashonaland, mai suna Mutsa Murombedzi ya kuma wallafa a shafinsa na X.

Kwanan sa biyar a dajin yana bacci kan duwatsu, ga kuma gurnanin zakuna da wucewar giwaye, babu abin da ya ke ci sai ‘ya’yan itatuwa.

Gandun dajin Matusadona dai na ɗauke da zakuna 40, akwai lokacin da ya kasance wuri mafi yawan zakuna a Afirka, kamar yadda bayanan African Parks suka bayyana.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda wata tawa Wani bature tatas saboda ya shiga gabanta a yayin da suke tsaye a layin banki a Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *