Tuesday, January 7
Shadow

Kamfanonin Sadarwa, MTN, Airtel da saransu sun mikawa gwamnati bukatar kara farashin katin waya dana data, suna son nunka kudin da suke caji

Kungiyar kamfanonin sadarwa sun nemi gwamnati ta basu dama su nunka kudin kati dana data.

Wakilin kamfanin MTN, Karl Toriola ne ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Arise TV yayi dashi.

Saidai ya bayyana cewa da wuya, musamman saboda halin matsi da mutane ke ciki Gwamnati ta amince da bukatar tasu.

Yace amma karin ya zama dolene saboda la’akari da kudin da suke kashewa wajan yin aiki da hauhawar farashin kayan masarufi da kuma karuwar yawan mutanen dake amfani da waya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda wani dan kasar China ya yayyaga kudin Naira saboda jin haushin an kulle masa kamfaninsa a Legas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *