Tuesday, January 7
Shadow

Obasanjo ya bayyana cewa a zamanin mulkin Marigayi shugaban kasa, Umar Musa ‘Yar’adua Dangote yaso Gwamnati ta sayar masa da matatar man Fatakwal data Kaduna amma ‘Yar’adua yaki yadda

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa a zamanin mulkin marigayi, Tsohon shugaban kasa, Umar Musa ‘yar’adua, Dangote ya so sayen matatar man fetur ta Kaduna da Fatakwal amma ‘yar’aduan yaki yadda.

Obasanjo da yake bayani ranar 2 ga watan Janairu ya zargi kamfanin man fetur na kasa, NNPCL da yaudarar ‘Yar’adua a wancan lokaci suka hanashi amincewa da dala Miliyan $750 da Dangoten yaso biya a wancan lokacin dan kula da matatun man fetur din guda biyu.

Obasanjo yace a wancan lokacin watau 2007, tuni har Dangote ya biya kudin, Dala Miliyan $750 amma ‘Yar’adua ya mayar masa da kudin yace Kamfanin NNPCL zai ci gaba da kula da matatun man.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Yanda wata Daliba a kasar Iran ta tube kayanta, ta yi Tumbur, haihuwar uwarta a tsakiyar makaranta saboda an mata hukunci kan shigar banza da ta yi

Obasanjo yace, ya saka baki dan kokarin ganar da shugaba ‘yar’adua kan lamarin amma sai bai fahimceshi ba ya nace akan matsayarsa na ba za’a sayar da matatun man fetur din ba.

Saidai a martani kan wannan magana ta Obasanjo, Shahararren lauya kuma me ikirarin kare hakkin bil’adama, Femi Falana yace, akwai lauje cikin nadi ne kan maganar sayar da matatun man shiyasa ‘yar’adua yaki amincewa a sayar.

Falana yace kamfanin dake son sayen matatun man fetur dina wancan lokacin mallakar Dangote Oil, da Zenon Oil, da Transcorp ne. Kuma farashin da aka sakawa matatun man an sayar dasu rababa sosai, wanda darajarsu ta kai dala Biliyan 5 amma an sayar dasu ko wani sashe nasu akan dala Miliyan $750.

Karanta Wannan  Tinubu Ya Himmatu Wajen Rage Raɗaɗin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki, Inji Minista

Falana ya kara da cewa, dailin hakane yasa kungiyoyin kwadagon na ma’aikatan bangaren man fetur NUPENG da PENGASSAN suka dake har sai da suka je yajin aiki akan basu yadda da sayar da matatun man fetur din ba wanda da matsi yayi yawa, Shugaba ‘Yar’adua ya soke cinikin aka mayarwa da kamfanin kudin da ya biya.

Falana yace yana matukar jinjinawa wadannan kungiyoyin kwadagon kan aikin da suka yi na kishin kasa inda ya nemi su doge akan hakan.

Yace hakanan cinikin bai bi ka’idar da ake bi wajan sayar da kadarorin gwamnati ba inda a doka, mataimakin shugaban kasa ne ya kamata ya kula da maganar sayar da kadarorin amma Obasanjo a wancan lokacin, yaki yadda mataimakinsa, Atiku Abubakar ya jagoranci sayar da matatun man inda da kanshi ya jagoranci sayar da matatn man.

Karanta Wannan  Bazan taba bayar da kudi dan yiwa mutane auren gata a mazabata ba saboda bana son ganin karin yara da yawa>>Inji Dan majalisar Tarayya, Bello El-Rufai

Yace wadannan matsaloli ne suka sa dole aka soke maganar sayarwa da su Dangote matatar man fetur din.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *