Friday, January 23
Shadow

Kwanaki kadan bayan da ya karyata labarin komawa PDP, An hangi tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a ofishin Jam’iyyar SDP

Tsohon gwamman jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya saka mutane rudani bayan da aka ganshi a hedikwatar Jam’iyyar SDP a ranar Talata.

Hakan na zuwane kwanki biyu bayan da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya karyata labaran da suka ce ya bar Jam’iyyar APC zuwa PDP.

Tsohon shugaban NIMASA, Ahmad Tijjani Ramalan ne ya wallafa hotunan zuwan El-Rufai ofishin SDP.

Ya bayyana cewa an yi zama tsakanin El-Rufai da SDP ne a kokarin da ake na yin hadaka dan samo hanyar yin nasara akan Jam’iyyar APC a zaben shekarar 2027.

Karanta Wannan  Kamfanin Multichoice dake da tauraron dan adam na DSTV ya rage farashi daga dubu 20 zuwa dubu 10 bayan da ya tafka asarar kudade saboda mutane sun daina kallo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *