Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, babu lungu da sako na kasarnan da ba’a shaida salon mulkinsa ba a Najeriya.
Shugaban ya bayyana hakane ta bakin me bashi shawara akan harkar sadarwa, Daniel Bwala a yayin da ake hira dashi a gidan talabijin na TVC.
Bwala yace shugaba Tinubu a yayin da yazo kan mulki akwai jihohi kusan 19 dake fama da matsalar karancin kudi wanda cire tallafin man fetur da Tinubu yayi gwamnati ta samu karin kudin shiga sosai yasa jihohin suka farfado daga hanyar talaucewa da suka kama.
Bwala ya kara da cewa, an samu ci gaba sosai kuma kowane lungu da sako na kasarnan sun shaida hakan.
Yayi kira ga gwamnonin dasu tabbatar da sun bayar da ci gaban da ake bukata a jihohinsu.