Tuesday, January 14
Shadow

Bama jin dadin yanda mutane suka fara yanke tsammani akan wutar lantarki ta Gwamnati suka koma samarwa kansu da wuta ta hanyar Sola>>Gwamnatin tarayya ta koka

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Gwamnatin tarayya ta koka kan yanda ake samun karuwan musamman kamfanoni da ma’aikatun gwamnati na samarwa kansu wutar lantarki inda suke dena amfani da wutar lantarki da gwamnati da kamfanonin rarraba wutar na Discos ke samarwa.

A wani rahoto da hutudole ya kawo muku, kun ji cewa sama da kamfanoni da ma’aikatun gwamnati 200 ne suka daina amfani da wutar gwamnati suka koma samarwa kansu wutar lantarki, saboda tsadarta da kuma rashin tabbas.

Da yake kokawa game da wannan lamari, ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa basa jin dadin yanda ake daina amfani da wutar ta gwamnati.

Yace wutar lantarki ta Gwamnati tafi karfi da tabbas dama sauki fiye da wutar lantarkin da kamfanoni da ma’aikatu suka koma samarwa kansu.

Karanta Wannan  Ina goyon bayan kudirin dokar canja fasalin karba da raba Haraji a Najeriya>>Inji Bishop Kukah

Ministan yace gwamnati na samar da wutar lantarki da yawa, kamfanonin rarraba wutar ne ke kin sayen wutar da yawa dan kaucewa bashi saboda basa karbar kudin wutar da yawa a hannun mutane da kamfanoni.

Saidai ministan yace nan gaba yana fatan wadannan kamfanoni da ma’aikatu zasu dawo amfani da wutar lantarki ta gwamnati idan suka gane gaskiyar cewa tafi tabbas fiye da wadda suke kashe makudan kudade suna sakawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *