Tuesday, January 14
Shadow

An zargi mutane 64 da yi wa wata matashiya fyaɗe a India

Wata matashiya ƴar shekara 18 daga jihar Kerala da ke kudancin Indiya ta zargi wasu maza 64 da yin lalata da ita tun tana da shekaru 13 da haihuwa.

Ƴansanda sun kama mutane 28 da ake zargi da hannu a lamarin kawo yanzu – mutanen suna tsare kuma ba su yi wani bayani kan lamarin ba.

Waɗanda ake tuhumar da ke da shekaru tsakanin 17 zuwa 47, sun haɗa da makwabtan matashiyar da kociyoyin wasanni da abokan mahaifinta, kamar yadda ƴansanda suka shaida wa BBC.

Matashiyar ta ba da rahoton cin zarafin da ta ke zargin an yi ma ta ne bayan wata tawagar masu ba da shawara da ke aiki ƙarƙashin wani shiri na gwamnati sun ziyarci gidanta.

Karanta Wannan  Ga Bashi daga Gwamnatin Tarayya: Zaka iya neman daga Naira Miliyan 3 zuwa 20

Lauyan da ke jagorantar kwamitin kula da jin daɗin yara na gundumar, ya shaida wa jaridar Indian Express cewa matashiyar ƴar wasa ce kuma ta halarci sansanonin wasanni daban-daban.

Ƴansanda sun ce ana zargin cewa an yi wa matashiyar fyaɗe sau uku a cikin shekaru biyar da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *