Tuesday, January 14
Shadow

An gargadi gaba dayan mutane miliyan 10 dake zaune a birnin Los Angeles su shirya ficewa daga garin saboda Wata guguwa na shirin hura gobarar dake kan ci ta mamaye duka garin

Rahotanni daga gobarar dake faruwa a birnin Los Angeles na kasar Amurka na cewa mahukunta sun sanar da duka mutanen dake zaune a birnin watau mutane miliyan 10 da su shirya ficewa daga cikinsa saboda wata guguwa ta doso garin tana niyyar hura wutar dake ci ta mamaye duka garin.

Mahukunta sun ce suna kan shirin ko ta kwana na faruwar lamarin me cike da hadari.

Zuwa yanzu dai gobarar ta kashe mutane 24 sannan ta kone gidaje sama da dubu 12 kuma ta tursasa mutane 100,000 barin gidajensu.

Hakanan dukiyar da gobarar ta cinye ta kai dalar Amurka Biliyan 150.

Karanta Wannan  'Ya kamata a ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a Najeriya'

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *