Wednesday, January 15
Shadow

Farashin litar mai a Najeriya zai sake haura naira dubu daya

Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya wato IPMAN, ta ce farashin litar man fetur a gidajen mai zai zarta naira dubu daya nan da kwanaki masu zuwa.

IPMAN ta ce karin ya zama dole sakamako karin farashin da hukumar fiton man fetur da sanya ido kan sayar dashi ta NMDPRA ta yi.

Alhaji Salisu Ten Ten, shugaban kungiyar dillalan man fetur ta Arewacin Najeriya wato IPMAN, ya shaida wa BBC cewa, a shekarun baya man fetur daga kasashen waje ake shigo dashi, sai gashi kuma bayan matatar man fetur ta Dangote ta fara aiki sai aka daina shigo da man.

Ya ce, ” A lokacin da ake shigo da mai daga kasashen waje akwai harajin naira 10 kan kowacce lita da duk wanda ya shigo da mai yake biyan hukumar NMDPRA, to a yanzu saboda an daina shigo da man sakamakon matatar mai ta Dangote sai dillan man suka daina biyan wannan haraji na naira 10 kan kowacce.”

Karanta Wannan  Muna kyautata zaton farashin man fetur zai sauka>>Inji 'Yan Kasuwar Man Fetur

“To amma a yanzu hukumar NMDPRA, ta ce dole sai dillalan da suke dauko mai daga matatar Dangote sun dawo da biyan wannan haraji da suke biya a baya.”

Alhaji Salisu Ten Ten, ya ce kafin a yi wannan kari farashin lita a deffo ya kai naira 913 ko 912.

” Masu deffo sun ce tun da kudin da suke siyan litar mai a kan naira 899 yanzu an kara musu naira 10 akai, to dama neman kofa suke suma su kara farashin man akan wanda suke bawa masu gidajen mai.”In ji shi.

Shugaban kungiyar dillalan man fetur ta Arewacin Najeriyar IPMAN, ya ce masu deffo sun kara kudi don haka masu gidajen mai ma dole su kara saboda farashi ya kau akan yadda suke siya ada.

Karanta Wannan  Ganduje ya goyi bayan kakakin APC kan rikinsa da Obi

Ya ce,” Babu ruwan matatar mai ta Dangote a akan batun karin farashin mai, harajin da hukumar fiton man fetur da sanya ido kan sayar dashi ta NMDPRA ne ya janyo tashin farashin, amma matatar mai ta Dangote har yanzu bata kara kudin man fetur ba.”

Alhaji Salisu Ten Ten, ya ce suna siyo mai akan naira 935 kan kowacce lita daga Deffo, to idan suka hada da kudin lodi dana dakon man akan yadda suka siya dole farashi ya tashi, tun da ko ba komai ai suma sa dan dora riba ko ya take, in ji shi.

Ya ce,” Bisa la’akari yadda abubuwa ke tafiya a cikin kasa a yanzu farashin man fetur musamman a jihohin arewacin Najeriya zai iya kai wa naira 1,040 zuwa naira 1,050.

Karanta Wannan  T-Pain na nufin wahala ta karamin lokaci, Tinubu zai sake cin zabe a 2027>>Inji Doyin Okupe

Rahotanni sun ambato cewa deffo-deffo a Nijeriya sun ƙara kuɗin litar man fetur zuwa naira 950 a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *