Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur, OPEC ta bayyana cewa, matatar man fetur ta Dangote tasa farashin man fetur ya karye a kasuwar kasashen Turai.
Rahoton yace, Matatar man ta Dangote ta fitar da Man fetur, da man jirgin sama da Gas da sauransu.
Rahoton ya kara da cewa, a baya Najeriya ta dogara ne kacokan wajan shigo da man fetur daga kasashen waje amma yanzu lamarin ya canja.
Hakanan matatar man ta Dangote ba kasashen Africa kadai take sayarwa da Man fetur din ba, hadda kasashen Asia da sauransu.
Ana sa ran a yayin da karfin mamatar da yawan kasashen da take fitarwa da man fetur ke karuwa, zata ci gaba da dakushewa kasuwar man fetur ta kasashen Turai Armashi.