Me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa ba zai taimakawa Gwamnatin Tinubu da shawarwarin gyaran tartalin arzikin Najeriya ba.
Ya bayyana hakane a wajan taron tunawa da babban lauya, Gani Fawenhinmi a jihar Legas.
Yace gwamnatin ta kasa samun wanda zai fito yawa mutanen Najeriya jawabi akan alfanu da dalilin tsaretsaren da ta kawo dake jefa mutane a matsalar matsin rayuwa.
Sarki Sanusi yace mutanen dake cikin gwamnatin abokansa ne amma kuma basu nuna girmama abotar tasu ba dan haka ba zai taimakawa gwamnatin ta hanyar tayar da komadar tattalin arzikin kasarnan ba.