Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana damuwa kan bukatar kungiyar NLC ta a biyasu mafi karancin Albashi na Naira N494,000.
Ministan yace idan aka biya wannan mafi karancin Albashin da kungiyar NLC take nema, za’a rika kashe Naira N9.5 trillion wajan biyan Albashi.
Ya kara da cewa kuma hakan zai jefa rayuwar sauran ‘yan Najeriya miliyan 200 cikin wahala.
A zama na karshe dai da aka yi tsakanin kungiyar ta Kwadago da Gwamnati an tsaya ne akan gwamnati zata biya Naira Dubu 60 a matsayin mafi karancin Albashi wanda kungiyar Kwadagon tace bata yadda ba.
Hakan yasa kungiyar tace tunda dai ba’a cimma matsaya tsakaninta da gwamnati ba, zata shiga yajin aikin sai mama ta gani daga ranar Litinin dinnan me zuwa.