Saturday, December 13
Shadow

Hukumar Federal Civil Service Commission ta sanar da daukar sabbin ma’aikata

Hukumar Gwamnatin tarayya ta Federal Civil Service Commission ta sanar da daukar sabbin ma’aikata wanda za’a cike guraben ayyuka da yawa.

Me magana da yawun hukumar Taiwo Hassan ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin.

Hukumar ta bukaci ‘yan Najeriya dasu cike bayanansu dan samun gurbin aiki da ake nema.

Shafin da za’a bi dan cike bayanai shine: https://recruitment.fedcivilservice.gov.ng

Shafin zai kasance a bude har nan da zuwa ranar 10 ga watan Maris.

Hakanan hukumar tace masu bukata ta musamman da masu nakasa ma na iya neman wannan aiki.

Karanta Wannan  Wani Dan siyasa ne yake sa ana Ghàrkùwà da mutane a Najeriya saboda yana son ya ci zabe haka sukawa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan>>Inji Gwamnan Edo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *