Thursday, April 17
Shadow

A daina kokarin mayar mana da kasar mu kasar bakaken fata, mu ba bakar fata bane>>Inji Kasar Libya

‘Yan kasar Libya sun fitar da sanarwa inda suka bayyana cewa, a daina kokarin mayar musu da kasarsu kasar Bakar Fata dan kuwa su ba bakar fata bane.

Sun fitar da wannan sanarwa inda suke martani da kungiyoyin agaji na Duniya ciki hadda majalisar Dinkin Duniya kan sanarwar da suka fitar dake cewa, ‘yan cirani su zauna a kasar ta Libya.

Kungiyoyin Doctors Without Borders, the UN refugee agency, da Norwegian Refugee Council duk sun nemi bakaken fata ‘yan Cirani dasu zauna a kasar ta Libya.

Saidai kasar ta Libya tace hakan na barazanar mayar da kasar ta bakaken fata.

‘Yan cirani da yawa ne dai ke bi ta cikin kasar ta libya dan ahiga kasashen Turai neman ayyukan yi.

Karanta Wannan  Donald Trump ya sha rantsuwa a matsayin shugaban Amurka na 47

A baya dai kasar Tunisia ta taba yin irin wannan magana wadda tasa aka soketa a matsayin nuna kyamar bakake.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *