
A jihar Ondo Hukumomi na binciken wani fasto me suna Peter James saboda zargin dirkawa yarinya me shekaru 13 ciki.
Yarinyar dai na daya daga cikin mas wake-wake a cocinsa.
Lamarin ya farune a garin Oke-Gburowo, dake karamar hukumar Odigbo, ta jihar.
Da farko dai jami’an Amotekun ne suka kama faston inda aka kaishi fadar sarkin garin kuma bayan gabatar masa da zargin da ake masa, ya amsa laifinsa
Saidai daga baya ya murzawa idanunsa kwalli yace cikin ba nashi bane.
Mahaifiyar yarinyar me suna Mrs. Victoria Bernard tace faston ya ki amsa laifinsa ne saboda yaga yarinyar na da nakasa.
Ta yi kira ga hukumomi da su amsar musu ‘yancinsu.