Sunday, September 13
Shadow

Kalli Bidiyon: Sojan Najeriya ya dauki hankula sosai bayan da yace kullun yana zuwa cire Naira dubu 7 a asusunsa na banki, yace sai me gadi ya tambayeshi me zai hana ya cire kudin duka ya huta?

Wannan wani sojan Najeriya ne da mutane da yawa suka tausayawa rayuwarsa.

Yace kullun yana zuwa ya cire Naira dubu 7 daga asusunsa na banki.

Yace me gadi ya tambayeshi me zai hana ya cire kudin sa gaba daya ya huta?

Sai yace masa lambar wayar mahaifiyarsa ce akan Asusun bankin, kuma duk sanda ya cire kudi daga asusun bankin tana jin alert.

Ta hakane take gane cewa har yanzu yana raye bai mùtù ba.

https://twitter.com/AsakyGRN/status/2005244588911452490?t=mW7jOcKEFiFLhwQEFjO51Q&s=19
Karanta Wannan  Ta bayyana a fili cewa, Gwamnatin Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ta dauki nauyin Fulanin da suka takura ma yankinmu a Mulkinsa>>Inji Kungiyar Kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *