A karin farko a tarihin birnin New York na kasar Amurka, sunan Muhammad ya shiga cikin sunaye 10 na farko da aka fi sakawa jarirai sabbin haihuwa a birnin.
Sunan Muhammad shine ya zo a matsayi na 9 da aka fi sakawa jarirai a birnin na new York city a shekarar 2023 da ta gabata.
Ba a birnin New York City bane kadai aka fi sakawa jarirai sunan na Muhammad, hadda ma biranen kasar Ingila da Wales sunan Muhammad na kan gaba da aka fi sakawa jarirai sabbin haihuwa.
Sunayen Emma da Liam ne suka fi shahara a birnin na New York City inda aka sakawa jarirai mata 382 sunan Emma sannan aka sakawa jarirai maza 743 sunan Liam.
Wadannan sunaye sun dade suna a matsayi na daya na sunayen da aka fi sakawa jarirai maza da mata a birnin inda sunan Emma tun shekarar 2017 shine a matsayi na daya da aka fi sakawa jarirai Mata sai kuma sunan Liam tun shekarar 2016 shin aka fi sakawa jarirai maza a birnin.