Wakar da matashin Arewa Og Abba yayi ta samu kudinka kawai ka kashe ta dauki ha kula sosai a wajan ‘yan kudu da Turawa da sauran sassan Duniya.
Itace ta zama wakar Hausa ta farko data watsu sosai har wadanda ba Hausawa ba suka rera ta suka yi Bidiyo da ita.
Manyan Mawaka da shahararrun mutanene daga Kudu daga wasu sassa na duniya suka hau wakar.