Friday, December 5
Shadow

A karo na biyu, NNPCL sun sake rage farashin man Fetur a Abuja da Legas kadai

Rahotanni daga Abuja da Legas na cewa, Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya sake rage farashin man fetur a garuruwan biyu da Naira 10.

Kafar The Cable ta ruwaito cewa ta lura a Abuja ana sayar da man fetur din akan naira N890 maimakon Naira 900, hakanan a Legas kuma ana sayar dashi akan Naira N865 maimakon Naira N875.

Kafar tace ta gudanar da wannan bincike ne a ranar Juma’a data gabata.

Hutudole ya lura Wannan ne karo na biyu da hakan ke faruwa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon wajan da aka ware za'a gina kabarin Shugaba Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *