Monday, December 16
Shadow

A karshe dai bayan shan ruwan Allah wadai, Gwamnatin tarayya na shirin yafewa kananan yaran data kai kotu bosa zargin cin amanar kasa

Babban lauyan gwamnati kuma ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) ya fara shirin janye karar da gwamnatin tarayya ta shigar akan kananan yara na cewa aun ci amanar kasa ta hanyar yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu ta hanyar zanga-zanga.

Awanni bayan da aka gurfanar da yaran su 32 dai Lauyan Gwamnatin ya bayyana bukatar karbar shari’ar daga hannun ‘yansanda.

Yace akwai abubuwan da suke son sake dubawa game da shari’ar.

Kotu ta dai bayyana cewa sai ranar 1 ga watan Janairu sannan za’a ci gaba da wannan Shari’a inda ta tura yaran zuwa gidan yari.

Saidai babban lauyan gwamnatin yace ya nemi a canja ranar ci gaba da wannan Shari’ar watau a matso da ita kusa.

Karanta Wannan  ZABEN 2027: Ba Muśĺim-Mùšĺìm Bà, Ko Mùmìñi-Mùmìñi Ne Ba Za Mu Zaba Ba, Inji Wani Fusataccen Ĺimàmi, Malam Abubakar Mai Imani

Wata majiya daga ma’aikatar Shari’a ta bayyanawa jaridar Punch cewa tuni shugaban ‘yansanda ya mikawa babban lauyan gwamnati da takardun shari’ar.

Sannan kuma majiyar tace babban lauyan na kokarin janye duka zarge-zargen da akewa yaran da gaggawa.

Sannan ana tsammanin zuwa sati me zuwa watakila ranar Talata za’a dawo a ci gaba da wannan shari’a dan janye zargin da akewa wadannan yara maimakon ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2025 da aka sanya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *