
Rahotanni dake fitowa daga tattaunawar kasar Iran da kasar Amurka akan shirin mallakar makamin kare dangi na kasar Iran din na cewa an samu sauyi.
Rahoton yace, a yanzu kasar Amurka ta amince kasar Iran ta ci gaba da inganta makamashin Uraniyum da zai bata damar mallakar makamin Nokiliya.
Saidai sharadi shine kada ta rika yin hakan da gaggawa kamar yanda take yi a yanzu.
Hakan na zuwane bayan da labarai suka bayyana cewa kasar ta Iran ta inganta makamin Uraniyum zuwa matakin kaso 60 cikin 100 wanda kiris ya rage mata ta kai matakin 90 cikin 100 wanda shine zai bata damar mallakar makamin kare dangi.
Hakanan a baya, kasar Iran ta rika yin watsi da bukatocin kasar Amurka na cewa ta daina inganta makamashin Uraniyum.
Wannan dai ba karamar nasara bace ga kasar Iran musamman idan aka yi la’akari da cewa a baya ana ganin karfinta hai kai ba ko har ana iya afka mata da yaki kan shirin nata na mallakar makamin kare dangi.