
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, wadanda mutum ya taimaka a rayuwa sune ke komawa suna zama makiyansa.
Ya bayyana hakane ranar Alhamis a wajan kaddamar da littafin da tsohon Ministan shari’a, Bello Adoke a Abuja.
El-Rufai yace shima ya taba kaddamar da littafinsa a baya inda ya bayyana irin yanda ya gudanar da aikin gwamnati har wasu na cewa yai kuskure dan a gwamnati ci ake a yi shiru.
yace amma bai yi dana sani ba.
Yace yaga yanda abokansa suka koma makiyansa sannan hakanan wadanda ya taimaka suka koma suka cutar dashi.
Ya jinjinawa Bello Adoke inda yace yana daga cikin wadanda suka karfafa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yadda ya karbi sakamakon zaben 2015.