
Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, a shekarar 1983, manyan sojoji sun sameshi suka ce zasu yiwa shugaban kasa a wancan lokacin, Shehu Shagari Juyin Mulki dan shi Obasanjon ya zama shugaban kasa.
Saidai Obasanjon yace musu baya so.
Yace dalilinsa shine su suka Kafa Dimokradiyya diyya a Najeriya dan haka ba zai zama cikin wanda zasu rusata ba.
Hakanan shima tsohon shugaban kasar Soji, Janar Ibrahim Badamasi ya tabbatar da wannan labari na Obasanjo.