
Bayan da Kungiyar kwallon kafar Najeriya, Super Eagles suka fito suka ce ba zasu buga wasan Algeria a gasar AFCON da ake bugawa a kasar Morocco ba saboda hakkokinsu da ba’a biya ba.
Gwamnatin tarayya tace an shirya tsaf dan biyan hakkokin na ‘yan wasan kuma zasu ya fara ganin Alert yau ko gobe.
Karamar Ministar kudi, Doris Nkiruka Uzoka Anite ce ta bayyana hakan a sanarwar data fitar.
Tace CBN ya fitar da kudin kuma an canjasu zuwa dala za’a Turawa kowane dan wasa zuwa Asusunsa na banki na Dala.