
Rahotanni sun bayyana cewa, a yau, Asabar, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara jihar Bauchi dan yiwa iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi gaisuwa.
Hakanan shugaba zai je jihar Borno dan kaddamar da wasu ayyukan da gwamnan jihar, Babagana Umar Zulum yayi, hakanan zai halarci daurin auren dan tsohon Gwamnan jihar ta Borno, Madu Sheriff.
Hakanan kuma shugaban zai wuce jihar Legas dan halartar wani bikin gargajiya.
Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan.