
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, a yau, Alhamis zai kafa sabon Tarihi da Tubalin ci gaban Najeriya wanda zai amfani har ma wadanda ba’a haifa ba.
Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ta kafar sada zumuntarsa inda yace yana godiya ga ‘yan Najeriya bisa hadin kan da suka bashi na canja fasalin Karbar Haraji a Najeriya.
Shugaban yace wannan sabon kudirin na Haraji zai habaka kasuwanci a Najeriya sosai domin akwai adalci a cikinsa.
Shugaban ya bayyana cewa, yana kira ga ‘yan kasuwa na Duniya cewa ga dama ta samu ta zuba hannun jari a Najeriya.
Ya kuma godewa, Kwamitin da ya kafa na canja fasalin karbar Harajin da majalisar dattijai da Gwamnatocin jihohi bisa gudummawar da suka bayar wajan tabbatar da canja fasalin karbar Harajin.