Friday, December 5
Shadow

‘Abin da ya sa muka zaɓi ADC a matsayin jam’iyyar haɗaka’ Su Atiku suka yi Bayani Dalla-dalla

A ranar Laraba ne manyan ƴan adawar siyasa na Najeriya suka tabbatar da amincewa da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin wadda za su yi aiki da ita domin tunkarar zaɓen 2027.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, wanda jigo ne a haɗakar ya ce: “mun kwashe wata tara zuwa shekara ɗaya muna tattaunawa domin ganin yadda za mu haɗa kanmu mu shiga jam’iyya ɗaya da ba za a iya soke rajistarta ba, mu gyara jam’iyyar da shugabancinta da aƙidarta da fito da tsarin da zai ceci ƙasarmu daga wannan hali da aka shiga.”

Hakan na zuwa ne bayan yunƙuri daban-daban da ƴan adawar suka yi na ganin sun samar da ƙwaƙƙwarar adawa da za su iya tunkarar shugaban ƙasar mai ci Bola Ahmed Tinubu, wanda suke zargi da gazawa a mulkinsa.

Ana iya cewa wannan mataki ya kawo ƙarshen raɗe-radi da hasashen da ake yi na hanyar da ƴan adawar za su bi domin tunkarar babban zaɓen na 2027 na Najeriya.

A baya ƴan adawar sun yi yunƙurin ganin an yi wa sabuwar ƙungiyar da suka fito da ita (ADA) rajista domin amfani da ita a matsayin lemar ƴan adawa.

Sai dai har yanzu hukumar zaɓe ta ƙasar INEC ba ta kammala dubawa ba balle ta sanar da amincewa ko rashin amincewa da bukatar ta ƴan adawa.

Da dama daga cikinsu sun zargi INEC ɗin da yunƙurin daƙile ƙoƙarinsu na kafa sabuwar jam’iyyar, lamarin da hukumar ta musanta.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Sadiya Kabala tace saurayinta yace kibarta ta yi yawa dan haka ta canja kalar abincin da take ci

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ce hakan ne ya sanya suka yanke shawarar neman jam’iyyar da ke da rajista a ƙasa domin ɗora tafiyarsu a kai.

“Mun yanke shawarar neman jam’iyya da ba ta da matsala mu shiga, amma ban da haka za mu ci gaba da ƙoƙarin rajistar sabuwar jam’iyyarmu, ko da gwamnati za ta yi ƙoƙarin ta shiga (ADC) ta kawo mana matsala.

“Wannan shigar mu ADC na wucin-gadi ne kuma idan aka samu jam’iyyar da ba ta da matsala” a cewar El-Rufa’i za su koma cikinta.

Sai dai Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa har yanzu bai bar SDP ba – wadda a yanzu ya yi zargin cewa “wasu shugabannin jam’iyyar sun riga sun zama ma’aikatan gwamnati…suna son su ɓata maganar SDP ta zama jam’iyyar haɗaka”.

Ɗaya daga cikin manyan zarge-zargen da ƴan adawar ke yi wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki shi ne haifar da ruɗani a cikin jam’iyyun adawa, duk kuwa da cewa shugaban ƙasar ya musanta hakan.

Ko a cikin bayanin da El-Rufa’i ya yi wa manema labarai bayan taron na ranar Laraba, ya ce “gwamnati ta lalata jam’iyyar PDP, ta kawo rudani a jam’iyyar LP da kuma NNPP.”

Sai dai ya ce a wannan karo ƴan adawar sun yi shirin yadda za su kauce wa hakan a jam’iyyar ADC.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ganin kare yana cin Bulo ya baiwa mutane mamaki

“A nan gaba ƙila mu canza wa jam’iyyar nan (ADC) suna, kila ma mu canza mata fasali, in kuma gwamnati ta ɓata ta dukkan mu za mu koma wata jam’iyyar guda ɗaya tak, da mabiyanmu da ƴan takarar,u domin a fuskanci wannan gwamnatin,” in ji El-Rufa’i.

A ranar bikin zagayowar dimokuradiyyar Najeriya da ya gabata dai, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kore yiwuwar mayar da Najeriya mai bin tsarin jam’iyya ɗaya, kamar yadda ƴan adawa ke zargi.

Sai dai ya ce “ina jin daɗin ganin ku (ƴan adawa) a tagayyare” tare da cewa ba zai taimaka musu su ɗinke ɓarakar da suke fuskanta ba.

Babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya PDP na fama da matsaloli na cikin gida, lamarin da ya kai har gaban kotu.

Sai dai a cikin makon na ta gudanar da taro inda ta bayyana cewa ta ɗunke dukkanin ɓarakar da take fama da ita.

Haka nan jam’iyyun LP da NNPP duk suna fama da matsalar rikici na cikin gida.

A baya-bayan nan jam’iyyar SDP da ta fara samun tagomashi bayan komawar tsohon gwamnan na jihar Kaduna, ita ma ta shiga jerin jam’iyyun adawa masu fama da rikici.

Wasu daga cikin ƴaƴan jam’iyyar na zargin shugabanta da wandaƙa da kuɗi, sai dai a cikin wata tattaunawa da BBC, Shehu Musa Gabam ya musanta zarge-zargen.

‘Mun yi wa kanmu faɗa’

Wata babbar ayar tambaya da ake ɗora wa haɗakar ƴan adawar ita ce yadda ake kallon cewa ta haɗa mutane daga jam’iyyu daban-daban masu buri ɗaya – wato shugabancin Najeriya.

Karanta Wannan  Na Rantse Da Kùŕ'anin Da Na Daura A Kaina Mauludin Manzon Allah SÀW Abu Ne Mai Kyau, Kuma Kaf Duniya Babu Wanda Zai Ce Min Maulidi Abu Ne Mara Kyau Na Yarda, Inji Fatima Batul

Wani abu da masu lura da harkar siyasa a ƙasar ke ganin cewa idan ba a yi sa’a ba, ko ba jima ko ba daɗe za a iya samun ɓaraka a lokacin da aka zo batun fitar da ɗan takara.

Yanzu haka mutane biyu da ake wa kallon ƙashin bayan haɗakar – Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da kuma Peter Obi na LP duk sun yi takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata, kuma ana ganin cewa yanzu haka ma take-taken kowannensu na nuna cewa suna son sake tsayawa takara.

Sai dai Nasir El-Rufa’i ya ce jigon hadakar tasu shi ne ajiye buri domin samar da nagartacciyar jam’iyya.

“Tun da muka fara zazzagayawa mun ce musu ku ajiye burinku mu zo mu yi jam’iyya ƙaƙƙarfa domin hada kai a kori wannan jam’iyyar da wannan gwamnati,” in ji El-Rufa’i.

Ya ƙara da cewa ” Rotimi Amaechi ya yi takarar shugaban ƙasa kuma ƙila yana son ya sake yi, Atiku Abubakar ya sha yin takarar shugaban ƙasa haka nan Peter Obi ya yi takarar shugaban ƙasa.

“Mun yi wa kanmu faɗa cewa ya kamata mu ajiye wannan maganar, mu kafa jam’iyya ƙaƙƙarfa… duk mai buri, a zo a bi ƙa’idojin jam’iyya, duk wanda Allah ya zaɓa a mara masa baya”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *