Wednesday, January 15
Shadow

Abin da ya sa na fice daga jam’iyyar PDP – Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto a Najeriya, Dalhatu Attahiru Bafarawa, ya sanar da ficewar shi daga babbar jam’iyyar adawa ta ƙasar – PDP.

Bafarawa ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ta ɓulla a yau Talata 14 ga watan Janairun 2025, wadda ya sanya wa hannu da kansa.

A cikin wasiƙar ficewa daga jam’iyyar, wadda ya rubuta wa shugaban jam’iyyar na ƙasa a ranar 8 ga watan Janairu, Bafarawa ya ce: “Na rubuto wannan takarda domin gabatar da matakin ficewa daga jam’iyyar PDP”.

Ya ƙara da cewa “duk da cewa wannan mataki, wanda na ƙashin kaina ne kuma ba mai sauƙi ba, na ɗauke shi ne sanadiyyar mayar da hankalin da na yi kan wani sabon babi na aiki na daban, wanda ya yi daidai da manufata ta bunƙasa al’umma ta hanyar ƙarfafa matasa.”

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ta PDP ke fama da matsaloli sanadiyyar rikice-rikicen shugabanci da kuma saɓanin ra’ayi na cikin gida.

Kwana daya kafin bayyana takardar ficewar Bafarawa daga jam’iyyar ta PDP, wasu ƴaƴan jam’iyyar sun gudanar da zanga-zanga a babban ofishinta da ke Abuja, sanadiyyar wata harƙalla kan sahihin sakataren jam’iyyar na ƙasa.

Karanta Wannan  An kama matashi dan shekaru 19 da ya kàshè dansa me kwana 3 a jihar Adamawa

Lamarin da ya zo bayan tsawon watanni da aka kwashe ana taƙaddama kan shugabancin jam’iyyar, wanda ake ganin gurbi ne na yankin arewa ta tsakiyar Najeriya, a maimakon halin da ake ciki yanzu inda shugaban jam’iyyar, Umar Damagum ya fito daga arewa maso gabas.

Duk da cewa PDP ita ce babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, ana ganin cewa rikice-rikice na cikin gida ya yi mata tarnaƙi, ta yadda ba ta iya sauke nauyin da ke kanta na sanya ido kan lamurran gwamnati mai ci ƙarƙashin jam’iyyar PAC.

Me ya sa Bafarawa ya fice daga PDP?

Ya zuwa yanzu, babbar hujjar hujjar da Attahiru Bafarawa ya bayar ta ficewa daga jam’iyyar PDP shi ne domin mayar da hankali kan jagorancin wata ƙungiyar bunƙasa matasa.

A cikin wasikar da ya fitar, Bafarawa ya ce: “A baya-bayan nan na mayar da hankali kan zuwa ga wata tafiya ta matasa, wadda ke da muradin ƙarfafa gwiwa, da bunƙasawa da kuma sauya rayuwar matasa, waɗanda su ne gashin bayan makomar ƙasarmu”.

Karanta Wannan  Babu ƙanshin gaskiya cewa sojojinmu na yin murabus - Rundunar sojin Najeriya

Ya bayyana cewa yanzu zai karkata ne kacokan ga harkokin tallafa wa matasan.

Sai dai batun ficewar Bafarawa daga PDP ya ɓulla ne kwana ɗaya bayan da wata kotu a Sokoto ta yi watsi da ƙarar da ya shigar yana ƙalubalantar zaɓen shugabannin jam’iyyar a ƙananan hukumomin jihar.

A cikin ƙarar, ya yi zargin cewa ba a yi wa ɓangaren da ki yi masa biyayya adalci ba.

A lokacin da ta yanke hukunci, kotun ta ce waɗanda suka shigar da ƙarar ba su da hurumin yin hakan, kasancewar ba su ne suka tsaya takarar ba.

Wannan tamkar wata manuniya ce kan yadda siyasar tsohon gwamnan ke ƙara rauni a jihar tasa.

Sannan akwai masu ganin cewa taƙaddamar da aka riƙa samu tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar, Aminu Tambuwal, ta ƙara raunana siyasar tasa.

Wane ne Attahiru Bafarawa?

Attahiru Bafarawa ɗaya ne daga cikin manya, kuma sanannun ƴan siyasa a Najeriya, wanda ya fito daga jihar Sokoto, a arewa maso yammacin ƙasar.

Karanta Wannan  Ya kamata ƴan Najeriya su sauya halayensu - Tinubu

Ya mulki jihar Sokoto a matsayin gwamna tsawon shekara takwas bayan komawar Najeriya kan tsarin dimokuraɗiyya a baya-bayan nan, daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Ya lashe zaɓen ne har karo biyu a ƙarƙashin jam’iyyar ANPP.

Sai dai Attahiru Bafarawa ya daɗe yana taka rawa a fagen siyasar Najeriya, tun daga lokacin da ya yi takarar ɗan majalisar wakilan tarayya a shekarar 1979 ƙarƙashin jam’iyyar GNPP, inda bai yi nasara ba.

Bafarawa shi ne wanda ya kafa jam’iyyar DPP (Democratic Peoples’ Party), inda kuma ya yi takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar a shekara ta 2007.

Haka nan Bafarawa ta taɓa yunƙurin tsayawa takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin jam’iyyar ACN, inda ya sha kaye a hannun Nuhu Ribadu a zaɓen fitar da gwani.

Haka nan ya taɓa yin wani yunƙurin na tsayawa takaran shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, inda a nan ma bai yi nasara ba.

A baya-bayan nan, Bafarawa ya bayyana aniyarsa ta daina tsayawa takara ko kuma karɓar duk wani muƙami na siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *