Friday, December 5
Shadow

ABIN FARIN CIKI: Jami’ar Musulunci Ta Madina Ta Ayyana Littafin Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo A Kololuwar Mataki

Daga Khalid Yusuf Sambo

Kamar yadda a ke ganin a hoton da ke kasa, shahararriyar Jami’ar nan ta Musulunci ta Duniya da ke Birnin Madinar Manzon Allah (S.A.W) ta ayyana Littafin:

ضوابط الجرح والتعديل عند الحافظ الذهبي

Wallafar Prof. Muhd Sani Umar R/lemo (Hafizahullah) a cikin jerangiyar littafan da za ta yi wa daliban da ke gurbin karatun Digiri na uku (Ph.D) Jarrabawa a cikinsa. Shi ne Littafi daya tilo na mutumin yankin kaf Afirka da ya samu wannan tagomaci.

Hakika wannan yana sake nuna karbuwar Littafin da ficensa a Duniyar ilimi. Da ma kuma Littafi ne da ba a shaida kamarsa a bangarensa ba. Littafin shi ne kundinsa na samun shaidar kammala matakin Digiri na biyu a Jami’ar Musulunci ta Madina, wanda a lokacin ya rabauta na samun koluluwar mataki da jinjina mafi girma a fanninsa.

Karanta Wannan  Akwai yiyuwar Farashin Gas na girki zai tashi

Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allah Ya kara wa wannan Babban Malami Lafiya da Albarka Allah Ya jikan mahaifansa Ya saka masa da Alkhairi.

Mai Rubutu:
Musa Muhammad Dankwano.
Sakataren Kwamitin Ilimi Na Dr. Muhd Sani Umar R/lemo.
23-02-2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *